Gwamnatin Tarayya ta sanar da sake dage wa’adin hada layukan waya da Lambar Zama Dan Kasa (NIN) har zuwa ranar 31 ga watan Maris na 2022.
A baya dai gwamnatin ta sanya ranar 31 ga watan Disamban 2021 domin rufe dukkan layukan da ba su hada layukan.
- Ministan Abuja ya kamu da COVID-19
- Sabunta izinin tuki: Daya ga watan Janairu KAROTA za ta fara kamen masu Adaidata Sahu
Sai dai a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da Sadarwa ta Kasa (NCC), Dokta Ike Adinde, da takwaransa na Hukumar Kula da Shaidar Zama dan Kasa (NIMC), Mista Kayode Adegoke suka fitar ranar Juma’a sun ce a yanzu gwamnati ta tsawaita wa’adin da wata uku.
A cewarsu, ya zuwa ranar 30 ga watan Disamban 2021, NIMC ta yi wa ’yan Najeriya sama da miliyan 71 rajista a cibiyoyi sama da 14,000 da ke fadin kasar nan.
“Bugu da kari, NIMC ta kafa irin wadannan cibiyoyin a kasashe 31 don yi wa ’yan Najeriya da ke can rajistar.
“Wannan samun karuwar masu rajistar da aka yi har suka kai miliyan 71 ya nuna irin hobbasar da Gwamnatin Tarayya take yi, wanda kuma abin a yaba mata ne.
“Mun yanke shawarar tsawaita wa’adin ne bayan bukatar hakan da jama’a suka yi, kuma hakan zai taimaka wajen hanzarta yin aikin,” inji sanarwar.
Ko a baya dai gwamnatin ta sha tsawaita wa’adin a lokuta daban-daban, saboda ta ce tana son ba mutane damar yin rajistar kafin a kai ga kulle musu layukan wayoyi.