✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kara wa’adin hada lambar NIN da layukan waya

Pantami ya ce an yanke shawarar ne saboda a ba dimbin 'yan Najeriya damar samun yin hakan.

Gwamnatin Tarayya ta sake dage wa’adin da ta diba domin hada lambar katin dan kasa (NIN) da layukan waya da karin makonni takwas.

Hakan dai na nufin za a ci gaba da yin rijistar har nan da ranar shida ga watan Afrilun 2021.

Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa yayin tattaunawa da Kwamitin Ministan na Kar-ta-kwana domin tabbatar da hada layukan da ya gudana a Abuja ranar Litinin.

Pantami ya ce an yanke shawarar ne saboda a ba dimbin ‘yan Najeriya da ma baki dake zaune a kan ka’ida a kasar damar samun yin hakan.

Ya zuwa yanzu dai akwai sama da mutane miliyan 56 da kamfanonin layukan waya suka sami nasarar hada lambobinsu da layukan wayoyin nasu.

Sanarwar ta ce, “Kowacce lambar NIN za a iya hada ta da akalla layuka uku zuwa hudu.

“An sami karuwa matuka a alkaluman da muka tattara, mun sami karin mutane miliyan 47 ya zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2021,” inji sanarwar.

Kazalika, sanarwar ta ce akwai akalla cibiyoyin yin rijistar katin dan kasa guda 1,060 a fadin kasa, yayin da su kuma kamfanonin wayar suka bude daruruwan cibiyoyin yin hakan a fadin kasa.

Ministan ya ce shirin rijistar na daga cikin shirin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na inganta tsaron kasa ta hanyar da kuma saukakawa mutane domin su sami hada lambobin cikin sauki.

A watannin baya ne dai Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Kasa (NCC) ta yi barazanar rufe dukkan layukan wadanda da suka gaza hada lambobinsu da lambar ta NIN bayan cikar wa’adin da ta dibar musu.