✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sake kara kudin wutar lantarki a Najeriya

Karin ya fara aiki ranar 1 ga watan Janairu ga dukkanin masu amfani da wutar lantarki

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta sake kara farashin wutar, wata biyu bayan ta kara shi a watan Nuwamban 2020.

NERC ta amince wa kamfanonin wutar lantarki 11 da ake da su da su yi wa dukkannin kwastomominsu karin farashin

Sanarwar da Shugaban Hukuamr, Sanusi Garba ya sanya wa hannu ta ce sabon karin farashin ya fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2021 zuwa 1 watan Yuni.

A watan Yunin 2021, kuma NERC za ta sake duba farashin tare da yiwuwar karawa a kan wanda ta yi a watan Janairu.

Karin farashin na wannan karon ya shafi dukkannin masu amfani da wutar lanatarki ne, sabanin na watan Nuwamban 2020 da aka yi wa masu samun ta na awa 12 a rana a fiye da haka.

Hukumar ta ce ta amince da karin ne bisa la’akari da hauhawar farashin kaya da kashi 14.9% a Nuwamban 2020, tashin Dala zuwa N370.4 a watan Disamba, da sauran matsaloli.

Idan ba a manta ba a watan Satumban 2020, ’yan Najeriya da kungiyoyin kwadago sun harzuka da karin farashin lantarki da NERC ta yi, lamarin da ya sa Gwamnati ta soke shi ta kuma hau teburin tattaunawa da su.

Daga baya a watan Nuwamba, aka dawo da karin bayan an yi wa masu samun wutar ta sama da awa 12 rangwame, su kuma masu samun ta na kasa da hakan aka tsame su daga cikin wadanda da karin ya shafa.

%d bloggers like this: