Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Imo ta tabbatar cewa wasu bata-gari sun kai hari a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Ehime Mbano a Jihar.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Imo, Orlando Ikeokwu, ya ce maharan sun kona motoci uku a ofishin, amma ba a samu asarar rai ba.
- Ganduje ya zaftare albashin masu rike da mukaman siyasa a Kano
- Real Madrid ta lallasa Liverpool, Man City ta samu nasara a kan Dortmund
- Direban Shugaba Buhari ya riga mu gidan gaskiya
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 8 sun sace 28 a Kaduna
“An kai wa Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Ehime Mbano hari, ba a samu asarar rai a bangaren ’yan sanda ba, ba a saci makamai ba, amma an kona motoci uku,” inji shi.
An kai harin ne kwana daya bayan wani kazamin hari da aka kai wa Hedikwatar ’yan sanda jihar da gidan yari aka saki sama da tsararru 2,000, da ake zargin kungiyar IPOB ne ta kai. Kungiyar dai ta musanta.
A harin na tsakar dare da ake zargin IPOB da kai wa ranar Lahadi da dare, an kona daukacin motocin da ke Hedikwatar ’yan sandan aka kuma cinna wa wasu gine-gine wuta, ciki da har da sashen binciken manyan laifuka da Rundunar inda a nan maka aka saki duk mutanen da ke tsare.
Majiyoyi sun ce maharan sun kuma kai wa sojoji farmaki inda nan ma suka kona motocin sojojin.
Kawo yanzu dai wasu daga cikin fursunonin da suka gudu sun koma gidan yarin.
Bayan harin na Owerri ne aka umarci Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya je can ya tabbatar an murkushe miyagun.
Washegari, ranar Talata kuma Fadar Shugaban Kasa ta sanar da Mataimakin Shugaban ’Yan Sanda, DIG Usman Alkali Baba a matsayin sabon mukaddashin Babban Sufetan ’Yan Sandan Najeriya.