✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake gurfanar da Magu

Dakataccen Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annaci (EFCC) Ibrahim Magu ya sake gurfana a gaban kwamitin da ke binciken…

Dakataccen Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annaci (EFCC) Ibrahim Magu ya sake gurfana a gaban kwamitin da ke binciken zarginsa da almundahana.

Sake bayyanarsa a gaban kwamitin na tsohon Mai Shari’a Ayo Salami na suza ne bayan kwamitin ya saurari bayanai daga manyan jami’ai da darektocin hukumar a ranar Alhamis da ta gabata.

Wasu daga cikin manyan jam’ian za su sake bayyana a gaban kwamitin a ranar Litinin, sauran kuma a ranar Talata domin mika takardun da kwamitin ya bukata daga garesu.

A ranar Juma’a Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da maye gurbin Magu da da Darektan Ayyukan EFCC Umar Mohammed har zuwa lokacin da kwamitin zai kammala aikinsa.

Sanarwar da mai magana da yawun Ministan Shari’a Umar Gwandu ya fitar ta ce “dakatarwar za ta ba kwamitin da shugaban kasa ya kafa damar gudanar da cikakken bincike”.

Fadar Shugaban Kasa ta bakin mai magana da yawun Shugaba Buhari, Garba Shehu, ta ce dakatarwar ita ce abu mafi dacewa duba da irin zargin da ke kan Magu domin ba shi damar wanke kansa.

Sanarwar Garba Shehu ta ce babu wani shafaffe da mai a yaki da rashawa na Gwamnatin Buhari, kuma dole jami’an da ke da alhakin kare dukiyoyin gwamnati su rika fuskantar bincike idan da zargi a kansu.

Tun a ranar Litinin da ta gabata jami’an hukumar tsaro ta DSS suka tisa keyar Magu zuwa gaban kwamitin da ke zamansa a Fadar Shugaban Kasa domin amsa tambayoyi.

Zarge-zargen da yake fuskanta, kamar yadda rahotanni suka nuna sun shafi badalakar kadarorin gwamnati da hukumar EFCC a karkashin jagorancinsa ta kwato daga hannun masu satar dukiyar kasa.

Takardar korafin na kuma zarginsa da sakaci da aiki da fifita wasu jami’an hukumar a kan wasu da kuma rashin da’a ga Ministan Shari’a Abubakar Malami.

Mako guda ke nan da Magu ke tsare a hannun jami’an tsaro yayin da kwamitin ke ci gaba da gudanar da aikinsa.