✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake dage zaben kananan hukumomin Ebonyi

Karo na biyu ke nan da ake dage zaben a cikin watanni uku.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Ebonyi (EBSIEC) ta age zaben kananan hukumomin da ta shirya a jihar daga ranar 15 ga watan Agusta zuwa 29.

Wannan shi ne karo na biyu da ake dage zaben a cikin watanni uku.

Shugaban hukumar, Barista Jossy Eze wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a babban birnin jihar Abakaliki, ya ce dagewar ta faru ne saboda barin daya daga cikin jam’iyyun da za su fafata a zaben ta gudanar da zaben fid da gwaninta.

“Dalilin da ya sa kenan lokacin da muka karbi umarni daga kotu bayan daya daga jam’iyyun ta bukaci a ba ta lokacin gudanar da zaben fid-da gwani muka ce ba za mu ki bin umarnin kotu ba.

“Hakan ne ya sa muka yanke shawarar sake dage zaben daga 15 zuwa 29 ga watan Agusta kamar yadda hukuncin kotun ya bukata”, inji Jossy.

Sai dai hukumar ta dage cewa ranar 10 ga watan Agusta ita ce rana ta karshe da jam’iyyun da za su shiga zaben za su mika ‘yan takararsu.