Gwamnatin Tarayya ta tsawaita ci gaba da rufe filayen jiragen sama don zirga-zirgar kasa da kasa har zuwa watan Oktoban bana.
Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), ta wata sanarwa da ta fitar ga masu ruwa da tsaki a harkar sufurin ta ce ba za abude filayen ba a ranar 19 ga watan Agusta kamar yadda aka tsara tun da farko.
Gwamnatin Najeriya dai ta dakatar zirga-zirgar kasa da kasa a filayen jiragen tun a watan Maris saboda annobar COVID-19, ko da yake a kwanan nan ta sake bude su domin cigaba da zirga-zirga a cikin gida.
Gwamnatin dai ta yi ta fuskantar matsin lamba daga kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki a harkar na dage haramci kan sufurin
To sai dai fatan basu na dawo da harkar sufurin ta kasa da kasa a Najeriya ta fuskanci tasgaro bayan sanarwar dage sake bude filayen daga watan Agusta zuwa Oktoba.
Sanarwar dai ta ce, “Gwamnatin tarayya ta tsawaita lokacin ci gaba da rufe filayen jiragen sama domin zirga-zirgar kasa da kasa sai dai ga jiragen da suke dauke da kayan agajin gaggawa”.
Ko da yake, sanarwar ta ce za a iya nema tare da samun izinin sauka da tashin jiragen dake dauke da kayan agaji, magunguna da kuma ragowar makamantar wadannan ayyukan.
Kazalika, dokar ta tsame injina matukar fasinjojin da ke kan jirgin ba za su sauka bad a kuma jiragen dakon kaya daga haramcin.
“Idan akwai bukatar yin hakan, sai a mika bukatar hakan a rubuce ga ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika”, a cewar sanarwar da Kaftin Musa Nuhu, babban daraktan NCAA.