Ministan Birtaniya, Simon Murray, ya ce yara ’yan gudun hijira kimanin su 200 sun bace bayan da an ba su mafaka a karkashin gwamnatin kasar.
Bincike da kuma majiyar jaridar The Observer a kasar sun nuna cewa, ana yi wa yaran dauki dai-dai ne a kan hanya inda akan tilasta musu shiga mota sannan a yi awon gaba da su.
- Majalisun jihohi sun yi watsi da kudurin bai wa Kananan Hukumomi ’yancin cin gashin kai
- Karbar katin zabe: Gwamnan Kwara ya bai wa ma’aikatansa hutun kwana guda
Murray ya fada wa Majalisar kasar a ranar Litinin cewa, yaran da lamarin ya shafa ciki har da mace daya da akalla ’yan kasa da shekara 16 su 13.
Ya kara da cewa, 176 daga cikin yara 200 da suka bace ’yan asalin Albaniyawa ne.
Bayanai daga yankin sun ce tun da fari ’yan sanda sun yi gargadin yiwuwar kai wa yaran da suka yi gudun hijira su kadai zuwa kasar hari.