✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace tsohon ciyaman da wasu mutum 10 a Taraba

A cikin kwanaki 10 mahara sun sace sama da mutum 10 a yankunan.

An sace tsohon Shugaban Karamar Hukumar Yorro ta Jihar Taraba, Mista Ishaya Dimas Dila tare da wasu mutum 10.

An sace tsohon shugaban karamar hukumar ne da wasu mutane biyu a kauyen Dila da ke karamar hukumar a ranar Lahadi.

Kazalika, ’yan bindiga  sun harbe mutum biyu a kauyen Kunini da ke Karamar Hukumar Lau.

Aminiya ta gano cewa an harbe mutanen biyu ne sakamakon turjiyar da suka yi wa ’yan bindigar.

Maharan sun kuma sake yin awon gaba da mutum takwas a kauyen Kunini duk a ranar Lahadi.

Bincike ya nuna cewa a cikin kwanaki 10 da suka gabata an sace mutane sama da 40 a kauyukan Dila, Pupule, Maraban Kunini da kuma Kunini da ke kananan hukumomin Lau da Yorro.

Kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ba a samu damar jin ta bakinsa ba game da lamarin.