’Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukumar Esan ta Tsakiya a Jihar Edo, Mista Waziri Edokpa.
’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu mutum 13 da ke aiki da wani fitaccen kamfanin tafiye-tafiye da ke binrin Benin na jihar.
- An yi garkuwa dan uwan Mataimakin Gwamnan Edo
- An yi garkuwa da malamin jami’ar Ondo a jihar Edo
- ‘Yan banga sun ceto mutum 5 da aka yi garkuwa da su a jihar Edo
- ‘Yan sanda sun kashe mai garkuwa da kama mutum 46 a Edo
An yi garkuwa da Edokpa wanda malami ne a Sashen Lisaafi na Jami’ar Ambrose Alli tare da mutum 13 din a ranar Juma’a a kan titnin Benin zuwa Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwar sun kashe direbar motar da mutanen ke ciki ne sannan suka yi awon gaba da su.
Har yanzu maharan ba su tuntubi iyalan wanda aka yi garkuwar da sun ba balle a san halin da suke ciki.
Al’amuran tsaro sun fara ta’azzara ne tun bayan da ’yan sanda suka kaurace wa aikinsu bayan zanga-zangar #EndSARS.
Mutanen jihar Edo na rokon gwamnati da ta yi wani abu wajen dawo da ’yan sanda kan manyan titunan jihar domin rage ayyukan masu garkuwa da mutane.
Sai dai kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Chidi Nwabuzor, bai dauki waya ko amsa rubutaccen sakon da wakilinmu ya aike masa ba.