✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace shugaban jam’iyyar PDP na Legas

An dauke shugaban jam’iyyar bayan wata ganawa da gwamnonin Jihar Oyo da Osun.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Legas, Mista Philip Aivoji.

Bayanai sun ce an dauke shugaban jam’iyyar ne a akan titin Lagos zuwa Ibadan da misalin karfe shida na yamma ranar Alhamis.

Sakataren watsa labarai na jam’iyyar, Hon Hakeem Amode ya tabbatar da sace shugaban na jam’iyyar.

Mista Amode ya ce an yi garkuwa da shugaban jam’iyyar ne lokacin da yake komawa gida bayan wata ganawa da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde da na Jihar Osun, Ademola Adeleke.

Ya yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnati a dukkan matakai da su tashi tsaye kan wannan lamari domin ceto shugaban jam’iyyar.