✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ‘sace’ dan Kwamishiniyar Ganduje

Aminiya ta rawaito cewa Abdurrahman Abdu Usman ya bar gida tun a ranar 17 ga watan Janairun 2022.

Yanzu haka dai iyalan Kwamishiniyar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Kano, Dokta Zahra’u Muhammad Umar suna cikin fargaba da tashin hankali na rashin sanin halin da dansu Abdurrahman yake ciki.

Aminiya ta rawaito cewa Abdurrahman Abdu Usman ya bar gida tun a ranar 17 ga watan Janairun 2022, da niyyar tafiya Katsina inda yake yi wa kasa hidima.

Sai dai tun daga lokaci ba a sake jin duriyarsa ba, kasancewar ba a same shi a kan wayar salularsa ba.

Haka kuma, lokacin da iyalan iyalan Kwamishiniyar suka je don nemansa a Katsina, an sanar da su cewa bai je can din ba.

Har zuwa yanzu dai babu wata hujja da za a iya cewa sace Abdurrahman aka yi kamar yadda majiyar Aminiya ta shaida mana.

Har ila yau, majiyar ta bayyana cewa ba a sami wani kira daga wasu mutane ba akan neman kudin fansa ko wani abu makamancin hakan.

Aminiya ta sami labarin cewa jami’an tsaro a Jihar Kano suna nan suna aiki don gano wurin da Abdurrahman yake.

Yayin da take tabbatar wa Aminiya labarin, Kwamishiniyar, Dokta Zahra’u ta ce kimanin kwana 11 ke nan babu labarin inda dan nata yake.

Za a iya cewa batun batan mutane a Jihar Kano yana kara yawa a ’yan watannin nan.

A kwanan nan ma, tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Hon. Isyaku Ali Danja ya bayyana cewa sai da ya biya Naira miliyan 40 kafin ya fanshi mahaifiyarsa, Hajiya Zainab, wacce masu garkuwa da mutane suka sace a gidanta.

Haka kuma, a karshen makon jiya aka kama Malamin Makarantar Noble Kids School da ke Kwanar Dakata, Abdulmalik Tanko, ya yi garkuwa da dalibarsa inda kuma daga bisani ya kashe ta bayan ya nemi kudin fansa Naira miliyan shida.

Lamarin dai ya janyo yin tofin alatsine daga al’ummar da dama.