’Yan bindiga sun sace wani Basaraken Fulani mai suna Alhaji Aliyu Abdullahi a kauyen Maganda da ke Karamar Hukumar Kagarkon Jihar Kaduna.
Hakan na zuwa ne kasa da kwana shida bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari tare da sace mutane 37 a kauyukan Jihar Kaduna.
- Ya kamata a fara hukunta ’yan siyasa masu ci da addini — El-Rufa’i
- DAGA LARABA: Yadda Son Mata Da Dukiya Ke Raba Zumunci
Basaraken, wanda ake kira da Ardon Makera, rahotanni sun ce an sace shi ne a ranar Litinin da misalin karfe 6:12 na yamma a kauyen Janjala, a kan hanyarsa ta komawa kauyen na Maganda.
Aminiya ta gano cewa Barasaken wanda shi ne Shugaban Fulanin Karamar Hukumar ta Kagarko, na kan hanyarsa ta dawo wa ne daga wani taro da masu rike da sarautun gargajiya kan hare-haren da aka kai wa yankunan a ’yan kwanakin nan, lokacin da aja sace shi.
Wani mazaunin kauyen na Janjala wanda ya ce sunansa Ishaq, ya ce, “Yau [Talata] da safe, wani da zai je Maganda a kan hanyarsa ta dawowa daga Janjala, ya ga babur din Ardon Makera a gefen hanya, kuma ana hasashen an sace shi,” inji shi.
Majiyar ta ce kafin a sace basaraken, sai da ziyarci wasu danginsa da su ma aka yi garkuwa da su ranar Larabar da ta gabata a wani sansani da ke kusa da garin na Janjala, kafin daga bisani ya wuce wajen taron.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai babu wata sanarwa daga ’yan sanda a kan batun.