✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace Bafaranshiya a yankin Neja Delta

Ana dai zargin ’yaj IPOB ne suka dauke ta ranar Alhamis

Wasu ’yan ta’adda a yankin Neja Delta ne sun sace ’yar kasar Faransa da ke aiki da wani kamfanin man fetur a kusa da yankin Bakassi wanda aka ba kasar Kamaru.

Ana dai zargin tsagerun da ke ayyuka a yankin, wadanda ke ikirarin zama sojojin ruwa na haramtacciyar Kungiyar ’Yan Awaren Biyafara ta IPOB ne suka sace ta.

Lamarin dai ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis a kusa da wani ruwa da ke garin Idabato a da ke Jihar Kuros Riba.

Rahotanni sun ce ana kyautata zaton matar, wacce ba a kai ga tantance ainihin sunanta ba tukunna, tana aiki ne da kamfanin mai na Perenco Oil and Gas.

Bincike ya nuna cewa an dauke ta ne daga cikin wani jirgin ruwa mai matukar gudu, lokacin da take kan hanya tare da sauran matafiya, a kan hanyarsu ta zuwa garin Ndian, wanda ke Kudu maso Yammacin Kamaru.

Sai dai da wakilimu ya tuntubi Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Kuros Riba, amma ta ce ba ta kai ga samun rahoton lamarin ba tukunna.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Alhassan Aminu ya ce, “Ina Abuja yanzu tukunna. Ka bari na tuntubi jami’aina kafin na ce komai a kai.”