✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace ɗan sanda a Bauchi

An sace shi ne cikin dare a gidansa da ke Karamar Hukumar Toro

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da wani jami’in dan sanda mai mukamin ASP a Karamar Hukumar Toro ta jihar Bauchi.

Mazauna yankin da dama da aka zanta da su sun ce garin na Toro ya shiga rudani a daren Juma’a a lokacin da ’yan bindigar da ba a tantance ko su wanene ba suka far wa garin inda suka yi ta harbe-harbe.

Hakan dai ya sa mutanen garin suka yi ta gudu dar domin tsira rayukansu yayin da ’yan bindigar suka ɗauki ɗan sandan.

Duk kokarin tabbatar da faruwar lamarin daha ’yan sanda ya ci tura, domin jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan, SP Ahmed Mohammed Wakil, bai dauki kiran wayarsa ba ko kuma amsa sakonnin kar-ta-kwanan da aka aika a wayarsa ba, har zuwa lokacin hada wannan labarin.

Amma wani babban jami’in dan sanda a rundunar da ba ya son a bayyana sunansa ya ce, “abin bakin ciki ne lokacin da aka yi garkuwa da wani babban jami’in, ana kokarin kubutar da shi, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.”

Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun isa garin ne da misalin karfe 9:00 na dare da yawansu dauke da manyan makamai da suka rika harbin iska sama don tsoratar da jama’a.

Lamarin satar mutane don neman kudin fansa da ake ta tafkawa a Karamar Hukumar Toro dai ya shafi harkokin tattalin arzikin yankin a ’yan kwanakin nan inda jama’a ke fargabar zuwa kasuwanci a yankin saboda fargabar yin garkuwa da su.

Yayin da yake mayar da martani game da lamarin, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Toro, Hon. Isma’il Haruna Dabo, ya yi allah-wadai da faruwar lamarin, tare da yin kira da a kwantar da hankula.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici musamman idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, tare da ba jama’a tabbacin ci gaba da yin aiki tukuru domin kawo karshen yanayin.

%d bloggers like this: