Gwamnatin Tarayya ta fitar da bayanan takardun fasfon wasu mutum da ta sanya wa takunkumin tafiye-tafiye na tsawon wata shiye saboda sun saba dokar kariyar COVID-19.
Aminiya ta gano cewa an sanya wa mutanen su 100 takunkumin ne saboda sun ki yin gwajin COVID-19 da aka wajabta wa duk wanda zai shigo Najeriya ne.
- Buhari ya bukaci hadin kan kasashen Afirka wurin yaki da ’yan ta’adda
- Zamfara: An cafke mahara a Fadar Sarkin Shinkafi
- ‘Na ga yadda ake horar da yara su zama ’yan bindiga’
- ‘Na yi nadamar mai da kaina namiji’
Gwamnatin Tarayya ta kashi lakobin sanya kafar wando da matafiyan da ke kakkauce wa dokokin da ta sanya na hana bazuwar cutar, wadda take sake kamari a Najeriya.
Sakamakon haka ne ta haramta wa ‘yan Najeriya 100 fita kasashen waje, saboda sun saba dokar.
A ranar Asabar kuma Kwamitin da Shugaban Kasa ya kafa kan yaki da COVID-19 ya fitar da bayanan takardun fasfon mutanen da hukuncin ya shafa.
Kwamitin ya kara da cewa haramcin da aka sanya wa mutanen ya fara aiki ne daga ranar 1 ga Janairu zuwa 30 ga watan Yuni, 2021.
Ya kuma ce an sanar da wadanda hukuncin ya shafa game da matakin da aka dauka a kansu na hana su fita daga Najeriya a tsawon lokacin.
‘Hukuman shige da fice bar da masaniya’
Wani mai sharhi a kan sufurin jiragen sama, Group Capt. John Ojikutu ya ce Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ce ke da alhakin fitar da sunayen wadanda suka saba dokar, a matsayinta na mai kula da iyakokin Najeriya
Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun Hukumar Shige da Fice (NIS), Sunday James, domin karin bayani, amma ya ce hukumar ba ta da masaniya a kan umarnin.
“Ni ma yau (Lahadi) na gani a shafukan zumunta. Sai na shiga ofis gobe (Litinin) zan san hakikanin halin da ake ciki,” inji shi.
Matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka ya sa kamfanonin jiragen sama sun shiga taitayinsu game da tarar Dala $3,500 da gwamnatin ta sanya ta hannun Hukumar NCAA mai kula da sufurin jiragen sama.