✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa ranar zaben kananan hukumomi a Gombe

Wakilan jam’iyyar APC da na manyan jam’iyyun adawa biyu — PDP da NNPP — ba su halarci taron ba.

Hukumar Zabe ta Jihar Gombe, GOSIEC, ta ayyana 27 ga watan Afrilun 2024 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar.

Shugaban GOSIEC, Alhaji Saidu Shehu Awak ne ya sanar da hakan a yayin wani taron shugabannin gamayyar jam’iyyun siyasa IPAC da aka gudanar a ranar Alhamis kan shirye-shiryen zaben da ke tafe.

Wannan dai na zuwa ne bayan sauke shugabannin riko na kananan hukumomin jihar da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya yi makonni biyu da suka gabata.

A cewar Alhaji Shehu, doka ta bai wa hukumar ta GOSIEC damar gudanar da zaben a cikin kwanaki 101 daga yau Alhamis, 18 ga watan Janairu, inda kowacce jam’iyyar siyasa mai rajista za ta iya tsayar da ’yan takararta.

Saidu Awak, ya kirayi dukkan jam’iyyun da suke da bukatar tsayawa takara da su gudanar da zaben fidda gwani na ’yan takararsu kafin lokacin gudanar da zaben.

Kazalika, ya yi addu’ar Allah Ya tabbatar da alheri da samun zaman lafiya a lokacin gudanar da zabukan na fidda gwani.

Shugaban gamayyar jam’iyyun siyasar ta IPAC na Jihar Gombe, Abubakar M Aliyu, ya ce a shirye suke da su shiga wannan zabe da za a gudanar da suke da tabbacin zai gudana cikin adalci.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, wakilan jam’iyyar APC mai mulki da sauran manyan jam’iyyun adawa biyu — PDP da NNPP — ba su halarci taron ba.

Sai dai an ruwaito cewa, wakilan jam’iyyar Labour da ADC da APGA da sauran kananan jam’iyyu wadanda ko ofis ba su da shi sun halarci taron.