✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa dokar hana fita a Jangebe

An gano cewa harkokin kasuwar garin da makwabtansa na taimaka wa ayyukan ’yan bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ayyana dokar hana fita a garin Jangebe bayan barkewar rikici  a yain mika wa iyaye daliban nan mata 279 da aka yi garkuwa da su.

Da yake sanar da dokar hana fitar daga maraice zuwa hantsi a garin, Kwamishinan Yada Labaran Jihar Zamfara, Suleiman Tunau Anka ya ce, gwamnatin jihar ta kuma rufe kasuwar garin na Jangebe har sai abin da hali ya yi.

“Sakamakon kazamin rikicin da aka samu a Jangebe baya an sako daliban, Gwamnatin Jihar Zamfara ta sa dokar hana fita daga yamma zuwa safiya a garin.

“Dokar ta fara aiki daga ranar Laraba, 3 ga watan Maris, 2021, don hana bazuwar karya doka da oda a garin.

“Kazalika hujjoji sun tabbatar cewa harkokin da ake yi a kasuwar garin da makwabtansa na taimaka wa ayyukan yan bindiga; saboda haka an rufe kasuwar har sai abin da hali ya yi’, inji shi.

Ya kara da cewa, “Gwamnatin Jihar a tsaye take, kai da fata wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummarta ta kowane hali.

“Da wannan sanarwa, ana kuma umartar Rundunar ‘Yan Sandan Jiar Zamfara da ta tabbatar da bin wannan doka sau da kafa.”