✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rushe gidan wadanda ake zargi da satar mutane a Kuros Riba

Gwamnatin jihar Kuros Riba ta rusa wani gini mallakin wani mutum da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a jihar.

Gwamnatin jihar Kuros Riba ta rusa wani gini mallakin wani mutum da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a jihar.

Kazalika gwamnatin ta kuma rusa wani ginin otal da ake zargin ana amfani da shi wurin ajiye kananan yara da ake ajiyewa saboda karuwanci.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa gine-ginen da jami’an tsaro na Operation Akpakwu suka jagoranci rusawa na cikin babban birnin jihar na Kalaba ne.

Hadin gwiwar jami’an tsaron dai ta kunshi sojojin ruwa da na sama da na ’yan sanda da na NSCDC da kuma masu ba gwamnan jihar shawara kan harkar tsaro.

Mista Henry Okokon, mai ba gwamnan shawara kan harkar tsaro ya ce an ruguza gidajen na daya daga cikin hanyoyin yaki da bata-gari a jihar.

A cewarsa, “Wanna na daga cikin irin ayyukan da rundunar tsaro ta Operation Akpakwu wacce gwamna Ben Ayade ya kafa domin yaki da aikata laifuka, musamman garkuwa da mutane.

“Za mu ci gaba da rusa irin wadannan gidajen. Gwamna ya gargadi dukkan wanda ke aikata laifin ko kuma ba su mafaka a gidan sa da cewa ya kauracewa yin haka ko kuma ya fuskanci fushin hukuma.

“Wannan gargadi ne ga duk mai aikata irin wannan laifin ko kuma yake da burin aikatawa a nan gaba don ya zama izina a gare shi,” inji shi.