✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rusa matattarar mashaya a Hayin Banki Kaduna

A makon jiya ne ’yan banga a Unguwar Hayin Banki da ke karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, suka rusa inda ake zargin matattarar mashaya  ce…

A makon jiya ne ’yan banga a Unguwar Hayin Banki da ke karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, suka rusa inda ake zargin matattarar mashaya  ce da ke unguwar, bayan sun zargi wurin da zama matattarar barayi da miyagun mutane.
Wakilin Aminiya ya ziyarci wurin, inda ya tattauna da Kwamandan ’Yan Bangan Auwalu Aliyu, wanda ya bayyana cewa, “Dalilin wannan rusau shi ne, ka ga ana kiran wannan wuri Laberiya Street, idan dare ya yi, ka zo wannan wuri za ka yi tsammanin kana Jamaica ne. Wurin ya zama matattarar barayi ne, suna fakewa suna shaye-shaye tare da wasu korarrun sojoji, suna kwace, suna fyade, suna fashi. Ko a makon jiya, wani sojan sama ya zo wucewa, yara suka ciro wukake za su kwace masa mota, sai Allah Ya kawo mu, muka yi dauki ba dadi da su. Allah Ya taimake mu muka ci nasara a kansu.”
Ya kara da cewa, shi ya sa suka kai kukansu wurin Mai ba Gwamna Shawara a kan Harkar Tsaro, Kanar Yakubu Soja (mai ritaya), inda suka sanar da shi cewa akwai matsala a Hayin Banki. “Nan da nan ya kai kukanmu wurin Gwamna, kuma da ma Gwamna El-Rufa’i ba ya wasa. Nan da nan aka hada mu da karamar hukuma, inda su kuma suka ba mu izini mu tashi wurin. Yanzu haka ma muna tare da jami’in karamar hukuma, wanda ya zo ya duba yadda za mu rusa wurin,” inji shi.
Ya ce  an ba su mako daya, su  tashi sai suka nemi karin lokaci aka kara musu kwana uku amma ba su kwashe kayansu ba. “Shi ne bayan lokacin da muka diba musu ya kare jiya da daddare, sai muka zo yau muna rusawa. Kuma mutanen gari suna goyon bayanmu, domin sun dame su. Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne, idan mun kama mai laifi a irin wannan wuri, sai irin wadancan sojojin su zo su ce dole sai an sake su, kuma mu ba za mu gane korarren soja ba,” inji Kwamandan.
Aminiya ta tuntubi shugaban masu shagunan, Abdul’aziz, wanda ya tabbatar da cewa an kawo musu takardar sanarwar tashi kuma su kansu wadannan miyagun mutanen suna damunsu. “An kawo mana takarda cewa za a rusa wannan wurin saboda muna zama ne ba bisa ka’ida ba, sai muka je karamar hukuma inda muka kai musu takardaunmu da kuma shaidar biyan kudi domin muna biya tun 1999. Sai suka ce mana za su ga ciyaman. Muna jiran karamar hukuma amma ba mu kara jin komai ba kawai sai da safen nan suka zo suka fara rusau saboda kwanakin da suka ba mu sun kare jiya. Maganar ’yan ta’adda kuwa, mu ma suna damunmu kuma muna yawan kai kararsu. ’Yan bangan Jarumai da Gora, mun san suna kokari sosai. Mun zauna da su don su bar mu mu ci gaba da kasuwancinmu, sai mu hada hannu da su, idan mun ga wadannan mutane sai mu kira su, su zo su kama su. Idan mun yi haka za a yi maganin wadannan miyagun mutane, mu kuma mu ci gaba da kasuwancinmu,” inji shi.