✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rusa Jabi Daki-Biyu bayan kwana biyu da gargadi

An fara da matattarar bata-gari kafin gidajen kwana

Jami’an kula da Muhalli na Birnin Tarayya Abuja (FCDA), sun kaddamar da rusau a unguwar Daki-Biyu da ke Gundumar Jabi a ranar Larabar, cikin rakiyar ’yan sandan kwantar da tarzoma da ’yan banga.

Aikin na zuwa ne bayan sa’a 44 da ba da gargadin a bar yankin, inda , a ranar Litinin aka sanya wa gine-gine da bacoci da kuma rumfunan kasuwanci da za a rusa alama.

Tun a farko wasu mazauna yankin da suka zanta da Aminiya sun yi zargin cewa jagororin al’ummar wajen ne karkashin Dagacin Daki-Biyu Malam Ishiyaku Lamushi suka gayyato FCDA zuwa yankin don rusa gine-ginen wadanda ba ’yan asalin Abuja ba ne.

Sun kuma zargi jagororin da yunkurin karbar Naira dubu 1 zuwa dubu 3 don yiwuwar hana aiwatar da aikin.

Sun hyi zargin cewa shugabannin sun yi irin haka, sannan suka rika karbar kudin ba da izinin mayar da abin da aka rusan, a wancan lokaci.

Dagachi ba shi da iko

Sai dai Sakataren Dagacin, Mista Andy Sanga ya musanta zargin, yana mai cewa Dagacin ba shi da masaniya a kan lamarin kuma ba shi da ikon hana hukumar ta gudanar da aikinta ko sa ta ta yi.

Wani makusancinsa, Injiniya Lawan Halilu Daura, ya ce dagacin ya bukaci jami’an hukumar su yi aikinsu tsakani da Allah a lokacin da suka kai masa ziyara a ranar Litinin bayan sun sa alamar a inda za a rusa.

Ya ce da alama kiran da basarken ya yi ya yi tasiri ganin cewa ba a bar wuraren bata-garin unguwar ba kamar yadda ya ce aka saba yi a baya ba.

A cewarsa a baya akan rusa wuraren sana’a da na kwanan jama’a amma ake barin wuraren masha’a da ake zargin suna kamun kafa a wajen manya.

Wuraren da aka rusa

Wuraren da aka rusa a ranar fako ta Laraban, sun hada da yankin Forest da Christ Guarden, yanki da ke da gidajen karuwai da ya ce adadinsu ya kai 200. Sai kuma filin kwallo da ke matsayin matattarar mashaya.

Ya ci gaba da cewa an kuma yi rusan ranar farkon a kira Mosquito Garden da ke matsayin maboyar bata-gari ciki har da ’yan fashi da makami.

Sai kuma wani gidan wasan kwaikwayo da aka fi sani da suna Nura pro.

Ya kuma rutsa da rabin kasuwar garin da ke kusa da Gidan Dagacin kafin a tsayar da aikin da misalin karfe 3 na rana da nufin sake komawa a ranar Alhamis da safe.

Da sauran aiki.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ana sarai ci gaba da rushe-rushen ta ranar Alhamis za ta faro ne a unguwar ’Yan-Lambu yankin da al’ummar Hausawa suka fi yawa.

Tuni mazauna yankin suka tashi daga wajen tare da cire rufin kwanon gidaje da na bacoci da kuma abubuwan da ke cikinsu tun a ranar Talata, kwana guda bayan an sanya wa alamar wuraren da za a rusa.

Akwai kuma karin wasu unguwannin kwana kamar Monkey Garden da 44 da Mango Tree da ke da nau’ukan kabilu daban-daban, da ba a kai ga rusa su ba tukuna.

Ana kuma hasashen aikin zai iya kaiwa zuwa ranar Juma’a kafin a karkare shi.

Wasu jama’a da dama da suka zanta da wakilinmu, sun yi korafin rashin sanin inda za su sa kansu bayan barin wajen da suka shafe shekaru suna zauna.

Masu harkan fanteka kuma na cin kasuwa na sayan kadarori cikin farashi mara kima, kamar yadda ’yan gwangon ke aikin cire kadarori da a ka bari.

Bayanai sun ce an dau matakin ganin ’yan bola ba su saci kadarorin jama’a ba ta hanyar gayyar manyan jagororinsu, da suka yi masu gargadi.