✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe shagunan magani 537 a Kano kan saba ka’ida

Kungiyar Masu Hadarhada Magunguna ta Najeriya (PCN) ta garkame kantunan sayar da magunguna 537 saboda aiki ba bisa ka’ida ba a Jihar Kano. Laifukan da…

Kungiyar Masu Hadarhada Magunguna ta Najeriya (PCN) ta garkame kantunan sayar da magunguna 537 saboda aiki ba bisa ka’ida ba a Jihar Kano.

Laifukan da kungiyar ta garkame shuganan a kai sun hada da rashin yin rijista sai sayar da magunguna masu hadari ba tare da kulawar kwararru ba; Akwai kuma rashin ingantaccen wurin adana magunguna da kuma harkar miyagun kwayoyi.

Shugaban kungiyar na kasa, Famasis Elijah Muhammad, wanda ya samu wakilcin Daraktan Sashen Dabbada Doka na kungiyar, Steven Esumobi, ya ce har yanzu akwai dillalan magunguna da ba su da ingattattun wuraren adana, wasu kuma suna fataucin haramtattun magunguna.

“Wasu rumbunan suna makare da magunguna masu hadari da miyagun kwayoyi da kan iya fadawa hannun ’yan ta’adda, wanda shi ke kawo karin tabarbarewar sha’anin tsaro” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa wadannan wurare na bayan fage suna ba da gudunmawa wajen yawaitar shaye-shaye da shan magunguna ba bisa ka’ida ba.

Tawagar ta gudanar da wannan aiki ne a kananan hukumomi 20 da matsalar ta fi kamari a Jihar Kano, kuma an yi shi ne da hadin gwiwa hukumar kare fararen hula ta ‘Civil Defence’.

Kungiyar ta kuma ba wa al’ummar jihar tabbaci cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ganin sahihan magunguna kadai ake siyar musu, su ma masu sayarwa za ta tabbatar sun yi aiki bisa ka’ida don samun al’umma mai koshin lafiya.