Gwamnatin jihar Sakkwato ta sanar da rufe Makarantar Sikandaren Kimiyya ta mata ta jihar da annobar amai da gudawa ta bulla, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa ran daliba biyu, 70 kuma suke kwance a asibiti.
Kwamishinar Ilimin Kimiyya da Fasaha ta jihar, Dakta Kulu Nuhu Abubakar ce ta bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai a ranar Juma’a.
- Dole a rika yi wa mahajjata rigakafi ko gwajin COVID-19 duk sati – Saudiyya
- ‘Babu mahalukin da ya isa ya karya Gwamnatin Buhari’
A cewarta, “Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya amince da a rufe makarantar na tsawon sati biyu har a ga yanda lamarin ya kasance ana fatan samu sauki tukuna.
“Daga cikin daliban da suka rasa ransu, daya ta fito daga Karamar Hukumar Rabah dayar kuma a Bodinga, muna yi wa mahaifansu ta’aziyar rashinsu,” in ji Kwamishiniyar.
Dakta Kulu ta ce dukkan yaran da suka kamu sun fito ne daga makarantun kwana da aka rufe dake kan iyakar jihar ta Sakkwato da wasu makwabtan jihohi saboda matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Ta yabawa Gwamna kan nuna tausayi ga daliban, inda ya kuma bayar da umarnin a cigaba da kula su har su sami sauki kafin a mayar da su ga mahaifansu.
Kazalika, ta yaba wa Ma’aikatar Lafiya da ta Ruwa kan matakin da suka dauka don ganin daliban sun sake samun lafiya.