Jami’ar Jihar Filato, da ke Bokkos, ta dakatar da dukkan harkokin koyarwa a makarantar har na tsawon kwanaki goma, bayan wani ƙazamin hari da aka kai ya sanadin kashe wani ɗalibi.
Ɗalibin wanda ke matakin aji biyu a fannin kimiyyar na’ura mai ƙwaƙwalwa ya gamu da ajalinsa ne ranar Juma’a sakamakon harin da wasu ɓata-gari suka kai harabar jami’ar.
- Uba ya rasu yana ƙoƙarin belin ’ya’yansa a ofishin ’yan sanda
- Sarki Bamalli ya naɗa ɗansa sabon Walin Zazzau
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Magatakardan Jami’ar, Yakubu Ayuba ya fitar a ranar Asabar.
Ya ce, “Bayan wani abin baƙin ciki da ya faru a Jami’ar Jihar Filato da ke Bokkos, a ranar Juma’a, 19 ga Afrilu, 2024; kuma bisa la’akari da illolin da wannan hari zai yi wa ɗalibai da ma’aikatan jami’ar, hakan ya sa hukumar gudnarwa ta ɗauki matakin rufe jami’ar na tsawon kwanaki 10 daga ranar 19 ga Afrilu, 2024.
Yakubu ya ce an ɗauki matakin ne don ba da dama na ganin yanayin tsaro ya inganta a jama’ar.
Kazalika, sanarwar ta ce an dakatar da jarabawar zangon karatu na farko, inda za a dawo ci gaba da rubuta ta a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayun 2024.
Ana iya tuna cewa, a Juma’ar da ta gabata ce wasu ’yan bindiga suka kashe aƙalla mutum 15 yayin wani hari da suka kai kananan hukumomin Mangu da Bokkos da ke jihar.