✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe hanya saboda zaben Gwamnan Ondo

Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya ta hana zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 12 na ranar Juma’a zuwa 6 ya yamma ranar Asabar a fadin Jihar…

Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya ta hana zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 12 na ranar Juma’a zuwa 6 ya yamma ranar Asabar a fadin Jihar Ondo.

Ta ce umarnin na daga cikin matakanta na tabbatar da doka da oda a lokacin zaben na ranar 10 ga watan Oktoba, 2020.

Kakakin Rundunar, Frank Mba, ya ce matakin zai “hana ’yan siyasa da masu neman tayar da fitina samun damar aikata miyagun ayyukansu da daukar makamai da miyagun kwayoyi sannan zai hana ‘yan bangar siyasa kawo wa zaben cikas”.

Sanarwar ta ambato shugaban Rundunar na kira a jama’ar Jihar Ondo su kwantar da hankulansu kuma su fito su zabi abin da suke so.

Ya ce, “An yi cikakken shirin tabbatar da tsaro a lokacin zaben” sannan ya ba su yi hakuri kan “takurar da hana zirga-zirgar ababen hawan za ta haifar, yana mai cewa an yi haka domin tabbatar da dimokuradiyya a Najeriya”.

Ya ce duk wanda aka kama yana saye ko sayar da kuri’a ko satar akwatin zabe ko kalaman nuna tsana ko wani abin da zai tayar da fitina ko shafar zaben, to zai fuskanci hukunci.