✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rufe gidajen burodi 206 a Yobe

Shugaban kungiyar masu gidajen burodi na Jihar ne ya tabbatar da hakan.

Akalla gidajen burodi 206 ne suka rufe gaba daya a Kananan Hukumomin Jihar Yobe 17.

Shugaban Kungiyar Masu Gidajen Burodi ta Najeriya, reshen Jihar Yobe, Alhaji Manu Maibiredi ne ya tabbatar da haka a zantawarsa da jaridar Daily Trust a Damaturu, babban birnin Jihar.

Ya alakanta hakan da hare-haren Boko Haram da annobar COVID-19 da tashin farashin kayayyaki da karancin takardun kudi da rashin tallafin gwamnati da cewa su ne kan gaba wajen matsalar.

A cewarsa, “Mun fada wani mawuyacin hali yanzu sakamakon matsalar rashin takardun kudi da rashin farashin kayayyaki da kuma rashin tallafin gwamnati ga masana’antum

‘‘Kafin zuwan Boko Haram da annobar COVID-19, akwai gidajen burodi sama da 106 a Damaturu kawai, ban da sauran Kananan Hukumomi. Amma yanzu haka wadanda ke aiki ba su wuce 33 ba.”

Ya kuma ce yanzu haka gidajen burodi da dama na fama da barazanar durkushewa baki daya saboda tsadar kayan hadi.

Ya ce a sakamakon hakan, mutane da dama sun rasa hanyoyin samun kudinsu na yau da kullum.

Maibiredi ya kuma ce, “Galibin kwastomominmu sun fi son burodi na N100 da N200 da N300 da kuma na N500, amma ba su da tsabar kudi, me kake tsammani?” in ji shi.

Sai dai Shugaban kungiyar ya zargi gwamnatin Jihar da rashin yin abin da ya dace wajen tallafa musu da bashi duk da bukatar hakan da suka sha gabatar mata.

“Mun rubuta wasiku zuwa ga Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Yobe da Sakataren Gwamnatin Jiha da kuma Ma’aikatar Bunkasa Tattalin Arziki da Samar da Aikin Yi, amma babu abun da aka yi a kai,” in ji shi.