Gwanatin Jihrar Borno ta rufe wasu banyan bankuna uku saboda rashin sabunta takardar mallakarsu a sassan Maiduguri, babban birnin Jihar.
Hukumar Kula da Tsara Gari ta Jihar Borno (BOGIS) da ta rufe bankunan ta ce ta sha gayyatar su amma suka ki amsa goron gayyatar.
- Wata mata ta kona al’aurar mijinta
- Nan gaba kadan za a sako Daliban Kagara —Gumi
- Dalilin ’yan mata na son auren mai mata fiye da saurayi
Babban Sakataren BOGIS, Injiniya Adam Bababe ya ce, “Mun rufe wasu bankuna sai idan sun cika bi dokokinmu, kafin a bude su. Yau mun rufe bankuna uku.
“Gwamnati na bukatar kudaden shiga da sabunta bayanai don samar da sahihin kundin bayanan gine-gine a Jihar Bonro,” inji shi
Ya ci gaba da cewa “Akwai takaici bankuna na bin dokar mallamar kasa da biyan haraji a wasu garuruwa, amma su ki yin hakan a Jihar Borno saboda tunanin cewa dokarmu ba ta ta karfi. Shi ya sa muka zo mu tabbatar da ganin ana bin ta.”
Ya ce Hukumar za ta dauki irin matakin a ka sauran bankuna da cibiyoyin hadahadar kudi da suka yi kunnen kashi a fadin Jihar.
“Yanzu mun ziyarci rassan manyan bankuna uku, amma ba bankuna kadai ake dubawa ba, ana duba gine-gine ne da rana.
“Masu wasu wuraren sun ki amsa gayyatarmu amma mun fara da gidjen mai sannan muka je gine-ginen kungiyoyin kasashen duniya da na cikin gida suke amfani da su a matsayin ofisoshi ko rumbuna kafin yanzu mu koma kan bankuna,” inji shi.
Ya ce jihar ta sauya tsarinta ba bayar da haya ko sauya amfanin gine-gine, yanzu sai da amincewar gwamna.
Ya ce hukumar ta gano cewa daga cikin kungiyoyi masu zaman kasansu na kasashen duniya da na cikin gida 183 da ke aiki a jihar, 21 ne kadai masu rajista.
Hukmar ta kuma rufe ma’ajiya 8 da wasu rumbuna ciki har da wasu mallakar wata kungiya mai zaman kanta ta kasar waje da kuma wata ta cikin gida.