An rantsar da Daniel Chapo a matsayin shugaban ƙasar Mozambique na biyar a wani biki da aka gudanar a birnin Maputo.
Aƙalla mutum 2,500 ne suka halarci bikin a wannan Larabar yayin da kuma a gefe guda magoyan bayan ’yan adawa suka gudanar da zanga-zangar lumana waɗanda jami’an tsaron da ake girke a harabar bikin suka yi wa shamaki.
- China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas
- Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.80 — NBS
Rantsar da Shugaba Chapo na zuwa ne bayan shafe watanni ana gudanar da zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 300, a cewar wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu biyo bayan zaɓukan ƙasar.
Daniel Chapo tsohon gwamna mai shekaru 48 na jam’iyyar Frelimo mai mulki, ya gaji Filipe Nyusi wanda ya yi wa’adi biyu na mulki ya sauka.
Jagoran ’yan adawar ƙasar ta Mozambique, Venancio Mondlane, tsohon dan jarida kana dan majalisar dokoki mai shekaru 50 ya yi tir da zaɓen da ya ce an tafka maguɗi.
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa da na Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló ne kawai suka halarci bikin rantsar da sabon shugaban.
Sai dai sauran ƙasashe da dama sun tura wakilai ciki kuwa har da ƙasar Portugal wadda ita ce ta yi renon ƙasar ta Mozambique.
A watan Disamba da ya gabata ne Majalisar Dokokin Ƙasar ta ayyana Mista Chapo a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Kasar da kashi 65.17, yayin da abokin adawarsa, Venâncio Mondlane ya samu kashi 24 na ƙuri’un da aka kaɗa.