✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano wata masana’antar wayoyin iPhone na jabu

An kama mutanen bayan da suka samu bayanan sirri.

Mahukunta sun kai samame wata masana’antar kera wayoyin salula samfurin iphone amma na jabu a Maputo, babban birnin kasar Mozambique.

Hukumomin kasar Mozambique sun ce sun kwace wayoyin iphone na jabu kimanin 1,165, tare da kama wasu mutum biyu ’yan China bisa zargin gudanar da masana’antar.

’Yan sanda sun ce ana zargin masu masana’antar da kera wayoyin iphone na jabu, amma dai wadanda ake zargin dai sun musanta aikata ba daidai din ba.

BBC ya ruwaito jami’an Hukumar Hana Fasa Kwauri ta kasar ta ce ta samu nasarar kama mutanen bayan da suka samu bayanan sirri.

Babban Daraktan Hukumar mai kula da birnin Maputo, Gino Jone, ya ce hukumarsa ta samu korafi game da zargin, inda suka kaddamar da bincike ba tare da bata lokaci ba.

Ya ce “bayan binciken da muka gudanar na tsawon mako uku, sai muka gano masana’antar.”

Ya kara da cewa, “wani gini ne da ake gudanar da masana’antar, ana kera wayoyin tare kuma da sayar da su a wani shago da ke yankin Alto-Maè.”