✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rantsar da gwamnatin rikon kwarya a Mali

Shugabannin rikon za su mulki kasar na wata 18 kafin su mika wa zababbiyar gwamnati

An rantsar da Bah Ndaw a matsayin wanda zai jagoranci sabuwar gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali a wani kwarya-kwaryar biki da ya gudana a babban birnin kasar, Bamako, ranar Juma’a.

Wani kwamitin wadanda suka yi wa tsohon shugaban kasar, Ibrahim Boubacar Keita juyin mulki suka kafa ne ya zabi Bah mai shekara 70 a duniya bayan sun kwace mulki a ranar 18 ga watan Agusta.

Ana sa ran sabon shugaban wanda tsohon soja ne zai jagoranci gwamnatin na tsawon watanni 18 kafin ya shirya zabe tare da damka ragamar shugabancin kasar ga sabon zababben shugaba.

Kazalika, an rantsar da jagoran sojojin da suka yi juyin mulkin, Kanar Assimi Goita a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa na rikon kwarya.

A yayin bikin wanda manyan sojoji da alkalai da kuma jami’an diflomasiyyar kasashen waje suka halarta, Babban Alkalin Kotun Kolin kasar, Boya Dembele ya bayyana kalubalen da yake gaban sabbin shugabannin a matsayin gagarumi.

Ko a ranar 20 ga watan Agusta sai da kasashe 15 na Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) suka kakaba wa kasar takunkumi a wani mataki na matsin lamba ga sojojin su mika mulki ga farar hula.

Juyin mulkin Mali ya zo ne a lokacin da kasar ke fama da zanga-zanga kan halin matsin tattalin arzikin da kasar ta tsinci kanta, tabarbarewar tsaro da kuma rashawa a kasar.