An rantsar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Farfesa Charles Soludo, a matsayin sabon Gwamnan Jihar Anambra, a wani kwarya-kwaryar biki a Gidan Gwamnatin Jihar ranar Alhamis.
Soludo, wanda aka rantsar tare da mataimakinsa, Onyeka Ibezim, ya karbi ragamar Jihar ne daga tsohon Gwamna, Willie Obiano.
- Matar tsohon Gwamnan Anambra ta tsinka wa matar Ojukwu mari a wajen rantsuwa
- Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga sama da 100 a Neja
Da yake jawabi jim kadan da karbar rantsuwar, Farfesa Soludo ya yi alkawarin fara aiki ba kama hannun yaro, inda ya ce nan da ’yan sa’o’i zai fara sanar da kunshin gwamnatinsa.
“Yau ce ranata ta farko a aiki. Na fara aiki ne da misalin karfe 8:55 na safe, kuma zan yi aikin akalla sa’o’i takwas yau.
“Mun shafe sama da wata daya muna murnar lashe zabe, yanzu lokaci aiki ne. Saboda haka, babu wani minti ko Kwabo da za mu bata da sunan sharholiya.
“Nan da ’yan mintuna zan sanar da sunan wasu jami’an gwamnatina, sannan zan fara wani muhimmin taro da Majalisar Tsaro ta Jihar Anambra,” inji Farfesa Soludo.
Gwamnan ya kuma yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, saboda kyale mutanen Jihar su zabi abin da suke so kuma aka tabbatar musu da shi.
Bikin dai ya samu halartar manyan baki, ciki har da Shugaban jam’iyyar APGA na kasa Victor Oye da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Uchenna Okafor da Sanata Victor Umeh da matar tsohon Shugaba ’yan tawayen Biyafara, Bianca Ojukwu.
Wata wasika daga gwamnatin jihar dai ta nuna cewa mutum 50 kawai aka gayyata, kuma ba a yi wani gagarumin biki ba.
An dai rantsar da Farfesa Soludo, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, a matsayin sabon Gwamna bayan ya lashe zaben da aka gudanar a watan Nuwamban 2021 karkashin jam’iyyar APGA.