Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) Akinwunmi Adesina ya karbi rantsuwar fara aiki a karo na biyu a wani biki da ya gudana ta fasahar bidiyo ranar Talata.
Shugabar Majalisar Gwamnonin bankin kuma ministar kasar Ghana, Kenneth Ofori-Attah ce ta jagoranci rantsuwar.
Mista Adesina wanda tsohon ministan harkokin noma ne a Najeriya ya samu sake darewa kujerar ne bayan ya lashe zaben da aka gudanar ranar 27 ga watan Agusta ba tare da hamayya ba kuma zai shafe karin shakararu a sabon wa’adin.
Kwararre a kan harkokin tattalin arziki, shugaban ya zama jagoran bankin ne ranar 28 ga watan Mayun 2015, kuma shi ne dan Najeriya na farko da ya rike mukamin.
- Yadda ‘yan kasashen waje ke juya farashin fulawa a Najeriya
- Buhari zai raba wa manoma tallafin Naira biliyan 600
- Adesina ya yi tazarce a Bankin Raya Afirka
Masana harkar tattalin arziki da dama dai na ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin a wa’adin mulkinsa na farko.
Kazalika, kafin a sake zaben nasa a karo na biyu ya fuskanci kalubale iri-iri da suka shafi zarge-zargen cin hanci da rashawa.
Bankin AfDB dai shi ne babban bankin hada-hadar kasuwanci da ya kunshi kasashen nahiyar 54 da ma wadanda ba na nahiyar ba guda 27.