✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rage wa ma’aikaci albashi saboda dadewa a bandaki

Rahoton wani mutum a kasar Taiwan ya janyo muhawara a kafafen sada zumunta na zamani  bayan rage masa albashi da aka yi, sakamakon dadewar da…

Rahoton wani mutum a kasar Taiwan ya janyo muhawara a kafafen sada zumunta na zamani  bayan rage masa albashi da aka yi, sakamakon dadewar da ya yi a bandaki lokacin aiki.

Fusataccen ma’aikacin wanda ake kira da suna ‘Mr. A.’, a kwanan nan ne ya wallafa muryarsa a shafin Facebook cikin takaici da kuma cizon yatsa.

Mr. A. ya bayyana damuwa saboda gibin da mahukunta kamfanin da yake yi wa aiki suka yi wa albashinsa na wata, sakamakon yadda ya dauki lokaci mai tsawo a duk ziyarar da ya kai wa bandaki a watan da ya gabata.

Ana tuhumar ma’aikacin ne da daukan tsawan lokaci na kimanin awa 49.5 a cikin bandaki, wanda ya yi daidai da yana yin awanni biyu kenan a duk rana, ba tare da masaniyar cewa daukan lokaci mai tsawo a wurin biyan bukata laifi ne ga mahukunta kamfanin ba.

Ma’aikacin wanda aka zaftarewa albashin ya wallafa labarin abin da ya faru a shafin Blame 2 Commune Facebook Group, inda yake tambayar wasu mambobin shafin shawara a kan yadda zai bullowa lamarin.

Ya bayyana cewa, ya yi aikin kwanaki 22 a watan da ya gabata, inda ya yi aikin awanni 195 kuma a ka’ida duk awa ana biyansa Yuan 160 (kudin kasar China) wanda ya yi daidai da Naira dubu 9 da dari 379.18 a kudin Najeriya.

Ya kuma fahimci cewa, an cire masa kudin Yuan 4,400 daidai da Naira dubu dari 2 da dubu 57 da dari 9 da 27, don haka yake son ya tuntunbi sashen kula da ma’aikata na kamfanin.

Mista A. ya samu labarin cewar hoton da kyamarar boye ta dauka ya nuna ya kwashe kusan awanni 54 na lokutan aiki a bandaki duk a cikin watan da ya gabata.

Tun bayan sanarwar, mahukuntan kamfanin sun amince da cewa ma’aikaci zai iya yin awa daya ne kadai a cikin bandaki duk rana, lamarin da ya sanya aka cire masa kudin awanni 27.5 daga cikin albashinsa.

Ya ce hakan bai dace a ce an cire adadin kudaden ba, inda har ta kai kamfanin na yi masa barazana kan ya ajiye aikinsa ya tafi idan bai zai amince da matakin da ya dauka ba.

Shi dai ma’aikacin ya ce, yana shirin mika korafinsa ga Kungiyar Kwadago ‘Labor Bureau’ amma iyayensa ba su amince da daukan matakin ba, inda suke nemi ya kwantar da hankalinsa ya ci gaba da rike aikinsa.

Wannan rahoton dai ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta na zamani, inda wasu suka fahimci lamarin da cewa tsawon fiye da awanni 50 da ma’aikacin ya rika shafewa a ciki bandaki lokutan sun wuce tunani, yayin da wasu kuma ke goyon bayan ya kai karar kamfanin ga hukumomin kasar.

“Wane kamfani ne zai dauki ma’aikaci aiki amma ya yi awanni 2 a duk rana?” kamar yadda wani ya yi martani.

“Kana aiki awanni 8 a rana, kwanaki 22 a wata, wanda hakan ke nuna ya yi kwanaki 6 a bandaki a wata kenan, wace ma’akata ce ba za ta rage albashin ba?”

Wani kuwa martani ya yi kan cewa, “Idan zaka iya zama a cikin bandaki na tsawan awanni 2 a rana, ina tunanin wajen da ya kamata mutumin ya tafi shi ne ba bandaki ba, sai dai ya wuce asibiti.”