✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rage farashin lantarki a Ghana

Gwamnatin John Mahama a Ghana ta rage farashin wutar lantarki sakamakon tallafin Cedi miliyan 300 da ta bayar don saukakawa talakawan kasar nauyin biyan farashin…

Gwamnatin John Mahama a Ghana ta rage farashin wutar lantarki sakamakon tallafin Cedi miliyan 300 da ta bayar don saukakawa talakawan kasar nauyin biyan farashin wutar lantarkin.
A karkashin shirin tallafin a yanzu, masu amfani da wutar lantarkin musamman masu karamin karfi, za su biya Pesewa 34 a kan ko wani mizani na wutar lantarkin, maimakon Pesewa 67 da suke biya a da, kamar yadda BBC ta bayyana.
Daga farkon wannan watan ne dai shirin ya fara.
Rage farashin ya biyo bayan korafin da al’ummar kasar ke yi cewa yana neman fin karfinsu da kuma alkawarin da shugaban kasar ya yi na cewa za a rage farashin.
A karshen watan jiya, jama’ar kasar sun fuskanci matsalar karancin wutar lantarki da ya tabarbarewa, a fadin kasar, ko a Accra, babban birnin kasar ya kasance babu wutar lantarki.
Sai dai gwamnatin kasar ta alakanta matsalar da hare-haren da ake kai wa wuraren hakowa da fitar da mai da iskar gas, a makwabciyarta Najeriya.
Wasu na ganin cewa rashin wutar ba zai rasa nasaba da irin dimbin bashin kudin iskar gas da Najeriya take bin kasar ba. Yayin da wasu kuma suke danganta al’amarin da matsalar rashawa da cin hanci da ke addabar mafi yawancin kasashen Afirka.
A baya dai kasar ta Ghana ta zamo wata abin misali wajen samun wadatar wutar lantarki a yankin Afirka ta Yamma.