✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An raba wa manoma buhunan taki 1000 kyauta

Babban Mataimaki na Musamman kan harkokin siyasa a ofishin mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Honorabul Wilson Iliya Yangye (Garkuwan Ghauta) ya rabawa manoma takin zamani buhuna…

Babban Mataimaki na Musamman kan harkokin siyasa a ofishin mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Honorabul Wilson Iliya Yangye (Garkuwan Ghauta) ya rabawa manoma takin zamani buhuna 1000 kyauta.

Honorabul Wilson ya yi rabon ne ga mutanen karamar hukumar Jama’a, musamman ga masu karamin karfi daga ciki.

Yayin da take mika buhunan takin ga shugaban kwamitin rabon, karkashin jagorancin Misis Cecelia Musa a Unguwan Garaje da ke Kafanchan, ya bayyana damuwarsa musamman kan irin mawuyacin halin da manoma a yankin suka shiga.

Ya yi fatan tallafin zai kai ga hannunsu don rage musu radadin halin kuncin da suke ciki da fatan za su yi amfani da shi a daidai lokacin shirye-shiryen noman bana.

Wilson Iliya ya kuma roki jama’ar yankin da su ci gaba da kiyaye dokokin gwamnati na hana zirga-zirga da kuma shawarwarin jami’an kiwon lafiya don taimakawa kansu da kuma gwamnati wajen dakile yaduwar cutar a cikin jama’a.

Bayan nan, ya kuma mikawa asusun tallafi na yaki da cutar Covid-19 na karamar hukumar Jama’a da tallafin kudi don ci gaba da taimakawa wajen yaki da cutar a yankin.

Lokacin da ake rabon takin zamanin