Shugaban gidauniyar zaman lafiya ta musulmi da ke Jos, Alhaji Saleh Zazzaga, ya yi kira ga jama’a da su kauracewa kalaman da ka iya tayar da yamutsi a cikin al’umma.
Zazzaga ya yi wannan jan kunnen sakamakon kokarin da wasu mutane ke yi na mayar da martani a kafafan yada labarai na zamani kan kalaman da shugaban wata Majami’a ta ’yan darikar Katolika ta mabiya Addinin kirista ya yi a jihar Sokoto, Matthew Kukah a sakonsa na taya murnar Kirsimeti da sabuwar shekara.
- Za mu gina Asibitoci 484 a kananan hukumomi 44 na Kano — Murtala Garo
- Gobara: Gwamnatin Kebbi ta bai wa ’Yan Kasuwar Sakkwato Tallafin N30m
Zazzaga, ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Jos na Jihar Filato, ya bayyana cewa, tun ba yau ba Kukah ya jima yana bayyana kalaman da basu dace ba, wanda hakan zai iya haifar da fadace-fadace da fitintinu na ba gaira ba dalili a fadin kasar nan.
Shugaban gidauniyar ya yi Allah-wadai da kalaman na Kukah, ya kuma bayyana cewa, ya karanta wata takardar gargadi da wata kungiya a jihar Sokoto ta aike masa tana mai kiransa da ya janye kalamansa, ya kuma bayar da hakuri ko kuma ya tattara komatsansa ya fice daga birnin na Shehu.
Zazzaga ya ce, faruwar irin wannan barazana ce ga zaman lafiya kasar nan, a yayin da mutane da dama suka rika mayar da martani daban-daban ta kafafen sadarwa na zamani wanda a cewarsa hakan na iya tayar da zaune tsaye.
A karshe ya yi kira ga al’ummar kasar nan da a zauna lafiya ta hanyar mutunta juna ba tare da la’akari da Addini ko kabilar da mutum ya fito daga cikinta ba.