✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nemi gwamnati ta tallafa wa wasan tenis

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta ware makudan kudi don bunkasa wasan kwallon tenis a kasa baki daya. Mai horar da kungiyar kwallon tenis…

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta ware makudan kudi don bunkasa wasan kwallon tenis a kasa baki daya.

Mai horar da kungiyar kwallon tenis ta ’ya’yan Fulani zalla wacce ake kira “Team Fulani” mai suna Koci Tobi ne yayi furucin yayin da yake tattaunawa ta musamman da Aminiya a Abuja, a makon da ya gabata.

“Babban kalubalen da ke fuskantar harkar wasan tenis a Najeriya shi ne karancin kudi. Muna da yara da suka kware da za su iya shiga gasa su yi nasara amma rashin kudin da za a dauki nauyinsu shi ne matsala. Saboda haka nake yin kira ga gwamnati ta zuba kudi masu yawa don bunkasa wasan tenis daga tushe”, inji shi.

Koci Tobi wanda ya jagoranci yaran Fulani da wadanda ba na Fulani ba zuwa kasashe da dama na duniya ya bayyana cewa kishi ne ya sa ya zauna a Najeriya yake horar da matasa wasan tenis.

Ya bayyana cewa dukkan abokansa da suka koyi wasan tenis tare duk sun koma Amurka da kasashen turai.

Amma ya ce shi ya yanke shawarar zama a Najeriya ne don ya bayar da gudunmawarsa ga ci gaban kasa.

Ya bayyana cewa zakulo matasa daga kananan hukumomi tare da horar da su tun daga tushe shi zai kai kasar nan ga gaci a wasan tenis.

Ya bayar da misali da sauran kasashen duniya inda ya ce haka kasashen suke yi har suka cimma burin da ake so a wasan tenis.

Ya kara da cewa babban kalubanen da yake fuskanta shi ne na rashin tallafi daga gwamati.

Inda ya ce da gwamnati za ta tallafa masa da yanzu ya wuce duk inda ake zato wajen bayar da horo ga ’yan wasa masu hazaka.

Sai dai ya jadadda kudurinsa na ci gaba da koyawa ’ya’yan fulani wasan tenis har su cimma burin da ake bukata.

Ya dage a kan cewa ya mayar da hankali kan ’ya’yan fulani ne don ya tallafa musu su cimma burin da suke so a fannin wasan tenis.