Ana fargabar fursunoni 900 ciki manyan mayakan Boko Haram da ’yan bindiga da wasu manyan masu laifi da ke tsare a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja, sun tsere bayan ’yan bidiga su kai hari a cikin dare.
A ranar Talata da dare ne mahara suka kai hari gidan yarin suna harbe-harbe tare da tayar da abun fashewa. lamarin da ya haifar da tashin hankali.
- Kurewar wa’adin Saudiyya: Zargin cuwa-cuwar biza ya dabaibaye NAHCON
- Za mu yi wa fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja yankan rago —Ansaru
A gidan yarin ne ake tsare da manyan masu laifi, ciki har mayakan Boko Haram da ’yan bindiga da manyan jami’an gwamnati da aka kama da laifi.
Wata majiya daga hukumar Sibil Difens ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun jikkata wasu jami’an gidan yarin.
Majiyar ta ce “An yi kutse a Gidan Yarin Kuje inda ’yan ta’adda suka yi amfani da abubuwan fashewa wajen kusten.
“Shin shiga ne da misalin karfe 10:05 na dare dauke da muggan makamai,” inji majiyar.
Da yake ganawa da wakilinmu, kakakin Hukumar Gidajen Yari, Umar Abubakar, ya ce maharan da ba a gano ko su waye ba sun kai wa gidan yairn hari ne da misali karfe 12 na dare.
Sia dai ya ce zuwa lokaacin ba su kai ga gano ko maharan sun saki wasu daga cikin fursunonin da ke tsare ba.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa wasu daga cikin wadanda maharan suka kubutar ’yan uwansu ne da ke tsare a gidan gayran halin.
Shi ma dai Mataimakin Ministan tsare-tsare, Kikiowo Ileowo, ya bayyana mana cewa ba za su yi saurin ba da wasu bayanai ba, amma al’umma su kwantar da hankalinsu, domin Jami’an Hukuamr Gidajen Yari da ’Yan Sanda, da na Farin Kaya sun hada guiwa domin shawo kan lamarin.
Idan dai ba a manta ba a ranar Talatan ne wasu ’yan bindigar suka kai hari kan ayarin motocin Shugaban Kasa Muhamadu Buhari a hanyar Daura, mahaifarsa.
’Yan bindiga sun kuma harbe wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda a Jihar Katsina CP Aminu Umar, wanda shi ne Kwamandan ’Yan Sandan na Karamar Hukumar Dutsinma.