✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An nada wa Sarki Sanusi rawanin zama Halifan Tijjaniya a hukumance

Zan yi aiki tukuru domin ci gaban Darikar Tijjaniya da kuma mabiyanta.

Babban Halifan Sheikh Ibrahim Niass, Sheikh Mahi Niass, ya nada wa Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II rawanin zama Halifancin Darikar Tijjaniya na Najeriya a hukumance.

Sashen Hausa na Jaridar Daily Nigerian ya ruwaito cewa, a watan Mayun bara ne dai aka gayyaci Sanusi zuwa Senegal, cibiyar darikar, inda a nan aka bayyana da shi a matsayin Halifan Tijjaniyya na Najeriya.

Da ya ke jawabi bayan yayin nadin a wajen bikin Mauludin Sheik Ibrahim Niass da aka gudanar ranar Asabar a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, Sarki Sanusi ya yi kira ga al’ummar musulmi da su sadaukar da kansu wajen bin Allah sannan kuma su dage wajen kwarara addu’o’in samun zaman lafiya a kasar nan.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya kuma sha alwashin cewa zai yi aiki tukuru domin ci gaban Darikar Tijjaniya da kuma mabiyanta.

Kazalika, Sanusi ya sha alwashin hada kai da duk wasu masu ruwa da tsaki wajen yada manufofin Tijjaniyya da kuma koyi da kayawawan dabi’un shugabanta Sheikh Niass.