Gwamnatin Tarayya ta amince da nadin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a matsayin Uban Jami’ar Kalaba, da ke Jihar Kuros Riba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin Jami’ar, Matthew Luther Agwai, ya fitar a ranar Laraba.
- An haramta yin dariya na tsawon kwana 11 a Koriya ta Arewa
- Cutar Zazzabin Lassa ta kashe likitoci 2 a Nasarawa
Ya ce hukumar gudanarwar Jami’ar na farin ciki da nadin Sarkin a matsayin Uban Jami’ar.
Agwai, ya ce gogewar Sarkin zai kawo ci gaba mai tarin yawa ga Jami’ar.
A nasa jawabin, Sarkin Aminu Ado Bayero, ya gode wa Gwamnatin Tarayya kan yadda ta martaba shi na nada shi a matsayin.
Ya ce, “Muna sane da yadda abubuwa suke a Jami’ar Kalaba a Jihar Kuros Riba, za mu tabbatar da samun ingantaccen ci gaba ta fagen ilimi.”
Kazalika, Sarkin ya bukaci hadin kai da goyon baya daga masarautar Kano tare da al’ummar Jami’ar don a kai ga gaci.
Har wa yau, ya bukaci hadin kan dukkanin masu ruwa da tsaki da kuma Hukumar Gudanarwar Jami’ar, don tabbatar da ci gaba mai dorewa.