Majalisar Gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Lafiya (FULafia), ta sanar da nadin Farfesa Shehu Abdur-Rahman a matsayin sabon Shugaban Jami’ar na uku a tarihi.
Shugaban Majalisar, Babban Farfesa Munzali Jibril ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamban 2020.
- Dan takara ya yi martani kan zanga-zangar adawa da aka yi masa a jihar Kano
- Yadda ake dakile matan Arewa a siyasa —Barista Sa’adat
- Majalisa za ta gayyaci Pantami kan matsalar rashin tsaro
Sanarwar ta ce, “an bi dukkan matakan da suka dace wajen zaben sabon Shugaban jami’ar kuma ana fatan zai yi riko da gaskiya da amana wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa domin kawo ci gaba a jami’ar.”
Gabanin wannan nadi, Farfesa Abdur-Rahman ya kasance Darekta a Cibiyar Nazari da Bunkasa Harkokin Noma (CARD) ta jami’ar kuma shi ne tsohon Shugaban Jami’ar Tarayya ta Gashuwa da ke jihar Yobe.
Farfesa Abdur-Rahman ya rike mukamin Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Noma kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa ta Keffi (NSUK).
Farfesa Shehu ya fito ne daga garin Umaisha na Karamar Hukumar Toto da ke jihar Nasarawa kuma zai karbi takardun kama aiki daga hannun Farfesa Muhammad Sanusi Liman a watan Fabrairun 2021.