✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada Magaji Galadima Mai Dawan Gombe

Bayan rasuwar Mai Dawan Jihar Gombe Mai Dawa Isah, da kimanin shekara 20, Babban Hakimin cikin garin Gombe da kewaye kuma Yeriman Gombe Alhaji Abdulkadir…

Bayan rasuwar Mai Dawan Jihar Gombe Mai Dawa Isah, da kimanin shekara 20, Babban Hakimin cikin garin Gombe da kewaye kuma Yeriman Gombe Alhaji Abdulkadir Abubakar, a makon nan ya nada Magaji Galadima, Galadiman Daji ya zama sabon Mai Dawan Jihar  Gombe.

Yeriman Gombe ya nada Magaji Galadiman ne a Mai Dawan bisa ga cancantar sa da wannan sarauta ta Mai Dawa na yadda ya jima yana harkar Farauta sama da shekara 30 kuma yana daga cikin na gaba gaban Yaran da Marigayi Mai Dawa Isah, yake alfahari da su.

Bayan tabbatar masa da wannan nadi na mai Dawan Gombe, Magaji Galadima, a zantawarsa da Aminiya ya nuna jin dadinsa matuka kan wannan nadi da aka ga ya dace aka masa ba tare da yaje ya roka ba.

Ya yi godiya ga Allah na yadda yana zaune a gida Yeriman Gombe ya tura aka kira shi aka ce ya je ya shirya an masa mai Dawan Gombe, sannan ya gode wa Yeriman na ganin cancantarsa da dacewar sa da wannan matsayi.

Cikin murna da farin ciki ya yi kira ga ‘yan Uwan sa mafarauta da cewa su zo a tafi tare a ciyar da harkar farauta gaba idan dama don Allah suke tunda a baya ma da babu mai Dawa ana harkar farautar tare ballantana yanzu da aka samu wanda zai ja musu gora.

“Mu kawar da hassada da kyashi, mu rungumi harkar mu ta farauta gadan gadan don mu gyara inda muke da kuskure sannan mu daga sunan Jihar Gombe a idon duniya, domin dama a harkar farauta muna sahun gaba,” inji Mai Dawa.

Ya kuma ce ba zai bai Yeriman Gombe da Masarautar Gombe kunya ba inda ya ce in Allah Ya yarda sai ya zama abun yin misalin da kowa yazo a bayansa zai rika koyi da shi.

Wani abu da ya ce ba zai manta da shi ba shi ne na yadda idan harkar farauta ta tashi a wani gari idan bai da kudi, ya ce yana iya daukar abincin gidansa ko wani abu da ya mallaka ya sayar don ya je wannan farautar.

Magaji Galadima, ya kuma ce a irin bajintar da ya yi a harkar farauta, ya taba harbe wata gada mai girman gaske wacce bayan ya harbe ta sai da ta ja shi da nisa kafin ya iya kayar da ita har ya yanka, inda ya ce wannan abu idan ya tuna yana matukar jin dadi.

Sanann sai ya yi godiya ta musamman ga mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III na yadda ya yi alkawarin basu hadin kai dan ganin an ciyar da harkar farauta gaba a jihar.

Daga nan sai ya yi amfani da wannan damar ya godewa manyan abokan farautar sa da a kullum suke ba shi shawara irin su Rabi’u Baushe Sarkin Bakan Bolari, da Barde Ibrahim Siza da Ali Alaye da Sanin Bakoji Ciroman Aska da sauran manyan mafarauta.