Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya nada kwamitin binciken gobarar da ta tashi a Juma’ar da ta gabata, kuma ta sake tashi a ranar Litinin a kasuwar katako ta Sango Igbajo a Ibadan.
Wata tukunyar iskar gas ce aka yi zargin ta haifar da tashin gobara ta farko a ranar Kirsimeti, a yayin da ake zargin wasu mutane da cinna wutar gobara ta biyu da gangan.
Babban Lauyan Gwamnatin Jihar, Mista Wasiu Gbadegesin, shi ne shugaban kwamitin mai wakilai shida da zai yi bincike domin gano musabbabin aukuwar gobarar da ta yi sanadin konewar shaguna fiye da 400 da injinan yankan katako manya da kanana da yankakkun falankin katakai masu yawa da motoci da injunan janareto da sauran kayayyaki na miliyoyin Naira.
Kwamitin binciken da aka nada a Talata, ya yi zaman farko domin ganawa da shugabannin kasuwar a ranar, inda ya fara sauraron koke-koken mutanen da al’amarin ya rutsa da su. Tun ranar Litinin da gobara ta biyu ta tashi ne wasu jami’an gwamnati a karkashin jagorancin mai ba Gwamna Shawara a kan Harkokin Sadarwa, Mista Yomi Layinka, suka ziyarci kasuwar domin gane wa idonsu asarar da aka yi tare da jajanta wa ’yan kasuwar.
A daidai lokaci ne shugaban ’yan kasuwar, Mista Rufus Oladapo Faseyitan, ya shaida wa jami’an cewa gobara ta farko ta tashi nedalilin fashewar wata tukunyar gas a wani gida da ke kusa da kasuwar, inda ya zargi wasu mutane da cinna gobara ta biyu dalilin jayayyar mallakar wani sashi na kasuwar.
Gwamna Ajimobi, ya umarci kwamitin ya yi bincike don gano ainihin abin da ya haifar da gobarar da irin barnar da aka yi da kiyasta asarar da ’yan kasuwar suka yi tare da bayar da shawara ga gwamnati, kan yadda za ta yi aiki wajen magance aukuwar haka a nan gaba da irin taimakon da za a yi wa ’yan kasuwar.
Gwamnan ya ce duk mutanen da ke zaune a kasuwar, su ne da alhakin samar da zama lafiya domin gwamnati za ta hukunta duk masu son tayar da hankali a cikin kasuwar.