✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada Hadiza Bala Usman shugabar hukumar NPA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Hajiya Hadiza Bala Usman a matsayin Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya, wato NPA.Hakazalika, ma’aikatar sufuri…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Hajiya Hadiza Bala Usman a matsayin Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya, wato NPA.
Hakazalika, ma’aikatar sufuri ta kasar nan ta sanar da cewa an nada wasu daraktoci uku da za su yi aiki tare da ita.
Sanarwar ta kara da cewa nadin na ta ya fara aiki ne tun ranar Litinin da ta gabata.
Kafin a ba ta wannan matsayi dai, Hajiya Hadiza, ta kasance shugabar ma’aikatan ta Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i.
Har ila yau, ita ce wadda ta kirkiro tare da taka rawa a kungiyar nan mai fafutukar ganin an ceto ’yan matan Chibok, wato Bring Back Our Girls, tun lokacin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan.
An haifi Hajiya Hadiza ne a shekarar 1976, a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Ta yi karatunta na digiri farko ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, inda ta karanta fanin nazarin kasuwanci, yayin da ta samu digiri na biyu daga Jami’ar Leeds da ke kasar Biritaniya a shekarar 2009.
Ta fara aiki ne a watan Yunin shekarar 2000, a matsayin jami’ar da ke kula harkokin bincike a wata cibiyar bincike mai zaman kanta da ke Zariya, mai suna Centre for Democratic Debelopment and Research Training (CEDDERT). Har ila yau, ta taba aiki da Hukumar Sayar da Kadadorin Gwamnati (BPE) tsakanin shekarar 2000 zuwa 2004.