A ranar Asabar da ta gabata ce aka nada dan uwan A’isha Buhari, Alhaji Musa Halilu Ahmed Sarautar Dujiman Adamawa.
Alhaji Musa wadda aka fi sani da Musa Yola wadda dan marigayi Alhaji Halilu Chiroma, Dujiman Adamawa na farko.
Lamidon Adamawa, Alhaji Dokta Aliyu Barkindo Mustapha ya umarci sabon Dujiman ya jagoranci jama’a tare da sanya tsoron Allah wajen gudanar da harkokinsa da kuma kara dagewa wajen taimakon jama’a.
Lamidon ya ce wannan lokacin da ya fi dacewa a nada sabon Dujiman domin sarauta ce da ba kowa ake baiwa ba sai wanda ya nuna kwazo da jajircewa wajen taimakon jama’a
Sabon Dujiman ya nuna godiya da kuma farin cikinsa game da wannan nadi, inda ya ce wannan matsayi da ya samu yin Allah ne ba yin sa ba kuma ya dauki alkawarin ganin cewa an samu ci gaba a jihar.
Alhaji Musa Halilu, shugaba a kamfanoni da dama wadanda suka shafi na noma da gine-gine da sauransu.
Daga fadar Sarki sai Dujiman ya hau dokinsa domin ziyartar Gwamnan Jihar Adamawa Muhammadu Umaru Jibrilla Bindow a gidan Gwamnatin Jihar, inda Gwamna ya ce lallai babu wanda ya dace da wannan sarauta sai shi domin ya nuna kwazo wajen ganin ci gaban jihar.
Sabon Dujima bayan kasancewarsa dan uwan A’isha Buhari yana auren ’yar marigayi Ardo Malabu Hammawa, Hajiya Amina Abubakar kuma Allah Ya albarkace su da ’ya’ya hudu.
Daga cikin wadanda suka halarci bikin akawi Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Gwamnan Jihar Adamawa Muhammadu Jibrilla Bindow da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da Janar Babagana Mungono da Ministan Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello da sauransu da dama.