✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An nada dan Sarkin Kuwait A Matsayin Fira Minista

Ahmad Nawaf Al-Sabah ya maye gurbin Fira Ministan Riko, Sheikh Sabah Al-Khalid, wanda ya yi murabus.

An nada Ahmad Nawaf Al-Sabah, dan Sarkin Kuwai, a matsayin sabon Fira Ministan Kasar.

Ahmad Nawaf Al-Sabah ya zama Fira Ministan Kasar ne a ranar Lahadi domin maye gurbin Fira Ministan Riko, Sheikh Sabah Al-Khalid, wanda ya yi murabus.

Ahmad Nawaf Al-Sabah shi ne Mataimakin Fira Minista kuma Minisatan Harkokin Cikin Gida a Gwamnatin Sheik Sabah Al-Khalid da ta yi murabus a watan Afrilu.

Sabon Fira Minsitan mai shekaru 60 ya fara aiki ne a hukumar ’yan sanda kafin daga bisani ya koma Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida.

Bayan mahaifinsa, Sheikh Nawaf Al-Ahmad, ya hau karagar mulki a 2020, sai aka nada shi a matsayin Mataimakin Shugaban Hukumar Tsaron Kasar.

A watan Maris aka nada shia Matsayin Ministan Harkokin Cikin Gida kuma Mataimakin Fira Minista.