✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An naɗa sabon shugaban Jami’ar Danfodiyo

Ya taɓa riƙe kujerar Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato.

Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato ta naɗa Farfesa Bashir Garba a matsayin sabon shugabanta.

Uban Jami’ar, Farfesa Attahiru Jega ne ya sanar da hakan a wannan Larabar a birnin Shehu.

Jega ya ce an naɗa Farfesa Garba sabon shugaban jami’ar bayan cimma matsaya kan fiye da mutum 10 waɗanda suka nuna sha’awar neman kujerar shugabancin jami’ar.

Bayanai sun ce kafin naɗinsa, Farfesa Bashir shi ne Shugaban Jami’ar Gwamnatin Jihar Sakkwato.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Farfesa Garba ya taɓa riƙe kujerar Sakataren Gwamnatin Sakkwato da zama Shugaban Makarantar Fasaha da Kere-Kere ta jiha.

Kazalika, Farfesan yana da ƙwarewa a aikin gwamnati.