An naɗa mace ta farko a matsayin mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya.
Appolonia Anaele mai muƙamin Laftanar Kanar ce za ta karɓi muƙamin daga hannun Manjo-Janar Onyema Nwachukwu.
- An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato
- Matashin da ya yi iƙirarin kashe mutane ya kai kansa ofishin ’yan sanda a Kano
Bayanai sun ce muƙamin nata zai fara ne a ranar Talata 22, ga watan Afrilun da muke ciki.
Shekaru sama da 50 ke nan da kafa rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya, kuma babu wata mace da ta taɓa riƙe wannan muƙami.
Duk da cewa kawo yanzu tana a matsayin mai riƙon muƙami ne, amma duk da haka wannan shi ne karon farko.