✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An mayar da ’yan Arewa saniyar ware a siyasar Legas – Faruk Magaji

Ko za ka bayyana mana mukaminka a Legas? Ni ne shugaban mutanen Arewa na karamar Hukumar Surulere a Legas kuma ni ne Otun Aro na…

Ko za ka bayyana mana mukaminka a Legas?

Ni ne shugaban mutanen Arewa na karamar Hukumar Surulere a Legas kuma ni ne Otun Aro na Jihar Legas, wato sarautar gargajiya ce da marigayi tsohon Oba na Legas wato babban basaraken jihar a wancan lokacin, Oba Adeyinka Oyeko ya ba ni. Sannan ni ne shugaban daliban Najeriya na Jami’ar Miyami ta Amurka a shekarar 1984.  Yau shekaruna 57, a Legas aka haife ni, hatta iyayenmu ma a Legas aka haife su. Kakanmu, Muhammad Bello Magajin Aska, ya zo Legas ne daga garin Tsangaya na karamar Hukumar Albasu ta Jihar Kano. A lokacin sana’ar wanzanci ce ta kawo shi Legas.

Ko me ya sa Oba ya ba ka sarautar Otun Aro na Legas kuma me wannan sarauta take nufi?

Sarautar Otun Aro na Legas babbar sarauta ce mai matukar muhimmanci. Oba na Legas na wanccan lokacin ya ba ni ita a shekarar 1995, a sakamakon gudunmowar da na bayar a Legas a fannin kiwon lafiya da ilimi, domin a lokacin a mulkin soji na Janar Sani Abacha, ni ne jami’in kula a fannin kiwon lafiya, sannan na yi wannan aiki a bangaren ilimi a nan Legas. A lokacin, duk da ni kadai ne dan Arewa ma’aikaci a Gwamnatin Legas, na taka gagarumar rawa don haka ne Oba na Legas ya karrama ni da wannan sarauta.

Ko ka gamsu da yadda ake ba ’yan Arewa aiki a gwamnatace a Legas ko wata dama a siyasance?

A gaskiya ko a can baya ’yan Arewa mazauna nan Legas ba sa samun wata dama a gwamnatance a nan Legas da ma can Arewar, inda in mutum ya je ake masa kallon bako; domin a wancan lokacin ko da makaranta ce ’ya’yan ’yan Arewa mazauna Legas suka tafi yi a Arewa ba a yadda cewa su ’yan Arewa ne. Sau tari sai in sun komo nan Legas sun sami takardar shaida daga wajen Sarkin Hausawa na wancan lokacin, marigayi Alhaji Dogara ko kuma mutum ya je ofishin jiharsa da ke Legas a yi masa takarda. Don haka a kowane lokaci nake ba jama’armu shawara, kowa ya bar gida, gida ya bar shi. Don haka mutanenmu su rka kokarin zuwa gida da ’ya’yansu akalla koda sau daya ne a shekara. Sannan wata matsalar koda mutum ya yi karatun boko, gwamnatin Legas ba ta ba ’ya Arewa aiki a ma’aikatunta, duk da yawan tarin matasanmu da suka yi karatun boko. Tun a wancan lokacin ne marigayi sarki Dogara ya yi kokari aka samu wasu Hausawa da ba su fi biyu ba aka dauke su a matsayin kananan ma’akata. Yanzu haka ma sun kusa yin ritaya. A gaskiyar lamari ’yan Arewa mazauna Legas na ba da gagarumar gudunmawa a fuskar siyasar jihar, sai dai ba su samun wani sakamako na a zo a gani, domin za mu iya cewa an mayar da mu saniyar ware a matakin jiha. A da can baya a kan tuna da mu, ana damawa da mu a siyasance, sai dai a yanzu babu wani abun a zo a gani da muka samu a wannan gwamnatin ta Akinwumi Ambode, idan ka kwatanta mu da ’yan kabilar Ibo, wadanda an dade ana ba su Kwamishina. Ko a siyasar 2015 kowa ya sani, su Ibo PDP suka yi amma bayan an kare siyasar su ne suke morarta, domin an ba nasu wata ma’aikata a tashar jiragen ruwa. Hakan ya ba shi damar ba Ibo guraben ayyuka amma mu a namu bangaren, wanda ake ganin ya samu wani abu wata ma’aikata ce ta kula da ruwan sha, babu kuma wasu ’yan Arewa da ke aiki da su, domin ba shi da damar yin haka.  Ka ga irin halin da ’yan Arewa suka samu kansu ke nan a Jihar Legas, ba su da wani tasiri, babu wani takamaiman jagora a siyasance wanda in sun samu matsala za su kai kukansu gare shi. A ’yan kwanakin nan ma sarkin Fulanin Jihar Legas, Alhaji Muhammadu Bambado ya yi irin wannan fashin baki na koma bayan ’yan Arewa a Legas a siyasance, a hirar da ya yi a wata kafar jarida, tabbas jawaban da ya yi su ne a zukatan mafi yawan al’ummar Arewa mazauna Legas. Maimakon hakan ya zama gyara ne da nusar da Gwamnatin Legas, sai aka samu wasu sun zo suna yin maganganun da ba su da tushe, suna cewa wai a baya shuwagabannin PDP sun kai masa ziyara. Ai shi shugaban jama’a na kowa ne, kowa na zuwa neman tubarraki da jama’a a wajensa, idan ’yan PDP sun je wajensa ai su ma na APC sun je.

Ko me kake ganin ya janyo wa ’yan Arewa a Legas koma baya a siyasance?

Babban abin da ya dushe tasirin ’yan Arewa a siyasar Jihar Legas shi ne rashin hadin kai, wannan babbar matsala ce ta sanya muka zama saniyar ware. Tabbas, laifunmu ne ’yan Arewa, domin duk inda aka ce maka babu hadin kai to ba za a taba samun ci gaba ba. A yanzu a Legas babu hadin kai a tsarin shugabanci na ’yan Arewa ta fuskar siyasa, sannan a bangaren shugabannin gargajiya ma akwai wannan matsala. Kowane mutum sai ya fito ya ce shi ne wane, shi ne sarki, bayan kowa ya san tushen sarautar Legas. To ka ga idan al’umma suka rasa hadin kai da jagoranci, dole a ci gaba da fuskantar matsala.