✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An mayar da harkar zabe kamar yaki a kasar nan – Safiya Daura

Hajiya Safiya Daura ita ce tsohuwar shugabar mata a tsohuwar Jam’iyyar CPC a Jihar Katsina, yanzu tana cikin jiga-jigan Jam’iyyar APC. A tattaunawarta da Aminiya…

Hajiya Safiya Daura ita ce tsohuwar shugabar mata a tsohuwar Jam’iyyar CPC a Jihar Katsina, yanzu tana cikin jiga-jigan Jam’iyyar APC. A tattaunawarta da Aminiya ta yi bayanin yadda suke shirin cin zaben 2015 da sauransu:

Aminiya: Yaushe kika fara harkar siyasa?
Safiya Daura: Tun ina sakandare na fara siyasa, kuma a Jamhuriya ta Biyu lokacin NPN na fara yin siyasa gadan-gadan. Sannan na shiga NRC, bayan na yi aure na koma Center Party. Da aka kara yin siyasa na shiga APP wadda ta zama ANPP, kuma muka kafa CPC sannan yanzu muka yi hadaka a APC.
Aminiya: Wace riba kika samu a siyasa?
Safiya Daura: Dama adawa nake yi, kuma kun san ’yan adawa kullum cikin wahala suke, kalli yadda wakilanmu suka bar mu, ko mota babu, kuma haka muke wahala da mutane, duk da haka zan ci gaba da siyasar. Na yi takarar shugabar mata a ANPP, yayin da aka kafa CPC ni ce shugabar mata a Jihar Katsina, kuma ko a yanzu ina zuwa tarurrukan kasa na APC.
Aminiya: Me za ki ce game da Jihar Katsina, jihar Janar Buhari, amma kullum PDP ke cin zabe a jihar?
Safiya Daura: Ai kullum kowa ya san mu muke cin zabe, tunda Janar Buhari ya shigo siyasa shi yake cin zabe, amma ba a ba shi. Musamman yadda ake siyasar Najeriya, idan ba ka da gwamnati a hannunka, kullum kamar yaki aka mayar da harkar zabe a kasar nan, a yi ne ko a mutu. Kuma ai ’yan sanda da hukumar zabe na da ikon karkata abubuwan da ke hannunsu.
Aminiya: Wani yunkuri kuke yi game da zabubbukan 2015?
Safiya Daura: Mutane kan manta da cewa kasar nan fa, kashin dankali ake yi, mu ne wadanda muke son gyara, yayin da ko makaho ya san abin da ake yi a kasar nan ba daidai ba ne, kuma ko yau za a yi zaben Allah da Annabi, mu za mu ci zaben. Bambancinmu da PDP shi ne, su suna da gwamnati a hannu, mu APC muna nema, amma idan yawan mabiya da masoya shi ne mulki, mulki na hannunmu. Wadanda ke waje su suke cewa muna da matsala, kuma siyasa ta gaji haka, ko babban gida ne sai ka ji ka-ce-na-ce. Kai ko abokai ne idan suka wuce uku sai ka ji wasu ko wani na tsegumi, amma maganar gwamnati mu muke cin zabe, kuma mu za mu ci zaben 2015, insha Allahu.
Aminiya: A karshe me za ki ce, idan ba Janar Buhari aka ba takara ba a Jam’iyyar APC?
Safiya Daura: Halin mutum jarinsa, kuma kowa ya san Janar Buhari bai taba cewa yana so ya mulki kasar nan ba, mu talakawa muke son ya tsaya takara don mu samu sauki. Domin kowa ya san halin da kasar nan ta shiga na talauci da cin hanci da rashawa da uwa uba rashin tsaro. Kowa ya san abin da ke faruwa a Arewa, ji abin da ya faru a Abuja, dubi Jihar Borno ko Gwamnan da kansa ya fito fili ya nuna halin da suka shiga, kai kanka ka yi tunanin a sace maka da, da ba kudi ba fa! Ko abokinka ne aka ce an sace, yaya za ka yi?
Aminiya: Ai ku ’yan adawa ke mulki a Bornon?
Safiya Daura: Duk abin da ake bukata Gwamnan Jihar Borno ya yi. Har sai da ya sa Naira miliyan hamshin kyauta ga duk wanda ya fadi inda ’yan matan nan suke. Idan da Gwamnan za a bar wa jihar da sai zaman lafiya ya dawo, dubi aikin da ya yi cikin wannan tashin hankalin. Amma Gwamnan ba shi ba ne Shugaban kasa, sannan an jibge sojoji a jihar, wadanda ba su karbar umarni daga Gwamna, yaya zai yi, ko kai ne yaya za ka yi?